Phelps na daf da lashe lambar yabo ta 26

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Juma'a za a yi wasan karshe a tseren mita 200

Dan kasar Amurka Michael Phelps na daf da lashe lambar yabo ta 26 jumulla a gasar Olympic a wasan linkaya.

Phelps ya kai wasan karshe a tseren mita 200 a gasar Olympic da ake yi a birnin Rio na Brazil.

Dan wasan wanda ya ci lambar zinare guda uku a Brazil, ya kai wasan karshe ne a tseren mita 200 a minti daya da dakika 55.

Phelps shi ne dan wasan da ya fi yawan lashe lambar yabo a tarihin wasannin Olympic, inda ya ci Zinare 21 da Azurfa biyu da kuma tagulla biyu.

A ranar Juma'a za a yi wasan karshe a tseren mita 200 a wasan linkaya na maza.

Labarai masu alaka