Nigeria za ta kara da Valencia

Image caption 'Yan wasan na gasar Firimiyar Nigeria za su kara da Valencia da Malaga da kuma Atletico Madrid

'Yan wasan gasar Firimiyar Nigeria za su kara da Valencia a wasan sada zumunta a ranar Laraba a Spaniya.

Karawar daya ce daga cikin wasannin da 'yan wasan gasar Nigeria za su yi da wasu kungiyoyin da ke buga gasar La Ligar Spaniya.

Bayan sun kara da Valencia za kuma su yi gumurzu da Malaga a ranar 12 ga watan Agusta, sannan ta kara da Atletico Madrid a Carranza World Club Tournament.

Tun a baya hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nigeria ta kulla yarjejeniya da ta La Liga domin yin aiki kafada da kafada.

Labarai masu alaka