Ranieri ya tsawaita zamansa a Leicester

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Claudio Ranieri ne ya fara kai Leicester har ta dauki kofin Premier League.

Kocin kulob din Leicester City, Claudio Ranieri ya amince da cigaba da kasancewa a kungiyar wasan har na tsawon shekara hudu.

Ranieri, mai shekara 64 dai ya jagoranci 'yan wasan na Leicester wajen cin kofinsu na farko na gasar Premier Ingila.

Yanzu haka, Claudio Ranieri ya bi sahun 'yan wasan kulob din kamar Kasper Schmeichel da Wes Morgan da Jamie Vardy wajen tsawaita zamansu a Leicester City.

Ranieri ya ce "Irin nagartar da 'yan wasan kungiyar da shugabanninta suke da ita da ma magoya baya, wani abu ne na musamman."

A ranar Lahadi ne dai Manchester United ta buge Leicester City da ci 2-1 a wasan Community Shield.

A ranar Asabar ne kuma Leicester za ta fara wasannin gabanin fara gasar Premier, a inda za ta je gidan Hull City.

Labarai masu alaka