An cire Mexico da Argentina a tamaula a Rio

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Korea ta Kudu ta kai wasan daf da na kusa da karshe a wasan kwallon kafa

An fitar da Mexico wadda ta lashe lambar yabo ta zinariya a wasan kwallon kafa da aka yi a Landan a shekarar 2012 daga wasan Olympic na bana.

Korea ta Kudu ce ta ci Mexico daya mai ban haushi a wasa na uku na cikin rukuni, inda Mexico ta kare a matsayi na uku a rukuni na uku da maki hudu.

Argentina ma an cire da daga wasan kwallon kafa da ake yi a birnin Rio na Brazil bayan da ta yi kunnen doki da Honduras.

Jamus ta kai wasan daf da na kusa da karshe, bayan da ta casa Fiji da ci 10 da babu ko daya.

Brazil mai masaukin baki za ta fafata da Denmark a ranar Alhamis, kuma sai kasar ta samu nasara ne za ta samu damar kai wa wasan zagayen gaba.

Labarai masu alaka