Olympic: An fitar da Serena a wasan tennis

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Serena ce ke mataki na daya a iya kwallon tennis a duniya

Serena Williams ta yi ban kwana da wasannin Olympic na bana, bayan da ta sha kashi a hannun Elina Svitolina a wasan kwallon tennis ta mata a wasan zagaye na uku.

William wadda ke mataki na daya a iya kwallon tennis a duniya ta yi rashin nasara ne da ci 6-4 da 6-3 a hannun Svitolina wadda ke mataki na 20 a iya wasan a duniya.

Svitolina za ta kara a wasan daf da na kusa da karshe ne da Petra Kvitova 'yar kasar Jamhuriyar Czech.

Tun a ranar Lahadi aka yi waje da Serene da Venus a wasan tennis ta mata biyu zalla, inda Lucie Safarova da kuma Barbora Strycova 'yan Jamhuriyar Czech suka doke su.

Labarai masu alaka