'Yan jarida ne suka juya kalamaina — Trump

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Donald Trump a cikin taron magoya baya.

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya zargi kafafen watsa labarai da iza wutar zargin da ake yi masa na hassala magoya baya da su kashe abokiyar takararsa ta jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton.

Ya shaidawa wata kafar watsa labarai cewa 'yan jarida marasa gaskiya ne suka juya kalaman nasa da suka yi nuni da cewa masu rajin kare hakkin mallakar bindiga za su iya hana misis Clinton hawa mulki ko da kuwa ta ci zabe.

Trump ya ce shi bai ingiza magoya baya ba illa dai ya nemi magoya bayan nasa da su fito su kada masa kuri'a.

Da yammacin ranar Talata ne dai Trump ya yi kalaman abin da kuma ya janyo suka daga mutane daban-daban.