Valencia ta ci 'yan gasar Firimiyar Nigeria 2-1

Hakkin mallakar hoto npfl twitter
Image caption nigeria za ta kara da Malaga da Atletico Madrid a wasannin gaba

Valencia ta samu nasara a kan 'yan wasan da suke buga gasar Firimiyar Nigeria da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka yi a Spaniya.

Valencia ce ta fara cin kwallo ta hannu Alvaro Medan a minti na 10 da fara kwallo, kuma saura minti 13 a je hutu Nigeria ta farke ta hannun Joseph Osadiaye.

Saura minti shida a tashi daga fafatawar Valencia ta ci ta biyu ta hannun Rodrigo Moreno.

'Yan wasan na Nigeria za su buga wasan gaba da Malaga da kuma Atletico Madrid a ranar 12 ga watan Agusta a Carranza World Club Tournament.

Nigeria na buga wasannin ne bayan da mahukuntan gasar Firimiyar kasa suka kulla yarjejeniya da na La Liga domin yin aiki tare.

Labarai masu alaka