Man United: 'Zuwan Pogba da Zlatan alheri ne'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wannan makon ne Pogba ya sauka a Manchester

Wasu masu ilimin kididdiga a jami'ar Salford sun yi wani bincike kan irin rawar da Manchester United zai taka sakamakon zuwan Paul Pogba da Zlatan Ibrahimovic kulob din.

Binciken ya nuna cewa 'yan wasan biyu za su sanya kulob din ya kara samun maki goma bisa wadanda ya samu, a kakar wasannin Premier da ta gabata.

A wannan makon ne dai Pogba, mai shekara 23 ya sauka a Manchester United a kan kudi £89m.

Shi kuma Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 34 ya baro PSG bayan da kwantaraginsa ya kare.

Labarai masu alaka