Murray ya kai wasan daf da na karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Murray zai kara da Steve Johnson a ranar Juma'a

Andy Murray ya kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar kwallon tennis da ake yi a wasannin Olympic a birinin Rio na Brazil.

Murray dan wasan Biritaniya ya kai wasan zagaye na gaba da kyar, inda ya doke Fabio Fognini na Italiya da ci 6-1 da 2-6 da kuma 6-3.

Da wannan sakamakon Murray zai kara da Steve Johnson na Amurka a ranar Juma'a.

Labarai masu alaka