Ingila za ta kara da Spaniya a Wembley

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sam Allardyce ne sabon kociyan tawagar kwallon kafa ta Ingila

Tawagar kwallon kafa ta Ingila za ta buga wasan sada zumunta da ta Spaniya a ranar 15 ga watan Nuwamba a Wembley.

Ingila wadda Sam Allardyce ke jagoranta za ta karbi bakuncin Spaniya, kwanaki hudu bayan ta kara da Scotland a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya na 2018.

Kamar yadda Ingila ba taka rawar gani ba a gasar kofin nahiyar Turai, ita ma Spaniya ta fice da gasar bayan da Italiya ta ci ta 2-0 a wasan zagaye na biyu.

Rabon da kasashen biyu su kara a wasa tun wanda suka yi a cikin watan Nuwambar 2015, inda Spaniya ta ci Ingila 2-0.

Labarai masu alaka