An kori wani kocin Kenya kan coge a Brazil

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mutane biyu aka kora 'yan Kenya daga Brazil kan batun amfani da abubuwa masu kara kuzarin wasa

An iza keyar wani dan Kenya kociyan mai wasan tsalle-tsale gida, bayan da aka same shi da laifin bayar da fitsarinsa don gwaji a matsayin dan wasa.

Kenya ta ce kocin, John Anzrah, ya gabatar da kansa a matsayin dan wasa a gaban wakilin da ke yin gwaji kan amfani da abubuwa masu kara kuzari, har ma ya saka hannu kan takardun shaida.

Anzrah shi ne na biyu daga Kenya wadanda aka tisa keyarsu zuwa gida, kan gwajin amfani da abubuwa masu kara kuzari, bayan manajan wasan guje-guje Michael Rotich.

An samu Rotich da laifin ankarar da masu horar da tawagar Kenya game da lokacin zuwan masu gwaji kan amfani da abubuwa masu kara kuzari, shi kuma a saka masa da fan 10,000.

Har yanzu ba a tantace dan wasan da Anzrah ke cewa yana horarwa ba, sai dai kuma wani bincike ya nuna cewar mutumin yana amfani da tikitin cin abincinsa domin karbar abinci kyauta.

Labarai masu alaka