Phelps ya ci lambobin zinare hutu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana sa ran Phelps zai iya lashe wata lambar yabon a ranar Asabar

Dan wasan Linkayar Amurka, Michael Phelps, ya lashe lambbobin zinare hudu a tseren mita 200 a gasar da ake fafata a birnin Rio na Brazil.

Dan wasan mai shekara 31, ya lashe lambobin Zinare guda 22 kenan jumulla a tarihin wasannin Olympic, yayin da daya dan Amurkan Ryan Lochte ya yi na biyar a tseren.

Bayan da Phelps ya lashe lambar zinare, Kosuke Hagino na Japan ne ya karbi lambar Azurfa, yayin da Shun Wang na China ya ci tagulla.

Ana sa ran Phelps zai iya lashe wata lambar zinare a wasan linkaya a ranar Lahadi.

Labarai masu alaka