An ba wa Mourinho hakuri kan Schweinsteiger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester United, Jose Mourinho

An ba wa kocin Manchester United, Jose Mourinho hakuri kan kiran da aka yi cewa ya kamata a daure shi a gidan yari dangane da abin da ya faru tsakaninsa da Bastian Schweinsteiger.

Dan kungiyar 'yan kwallon kafa na kasar Slovenia, Dejan Stefanovic ya fadawa BBC cewa Mourinho ya wulakanta dan wasan dan Jamus, a inda ya fada masa cewa da ya nemi wani sabon kulob.

Shugaban kungiyar manajojin kungiyoyin gasar Premier Ingila, Richard Bevan ya ce kalaman ba su kamata ba.

Sai dai kuma kungiyar ta manajojin kungiyoyin gasar Premier ta ba wa Mourinho hakuri kan kiran da aka yi da a daure shi a gidan yari.

Labarai masu alaka