Man Utd: Dalilin biyan £89m kan Pogba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paul Pogba tsohon dan wasan Manchester United ne.

Manchester United ta sayi dan wasan Juventus, Paul Pogba a kan £89m, dan wasan da Manchester United din ta saki shekara biyar da ta gabata a kan £1.5m kacal.

Wasu dai na yi wa cinikin kallon almubazzaranci a harkar wasan kwallon kafa.

Tsohon manajan kulob din Sir Alex Ferguson ya bayyana al'amarin da babban kuskure.

To amma a wata mai kamawa ne ake sa ran kulob din na Man United zai sanar da kuɗin shigarsa na shekara da suka kai yawan £500m.

Saboda haka kashe £89m wajen sayen babban dan wasan tsakiya ba wata matsala ba ce.

Kuma idan aka yi la'akari da kudin da aka zuba wajen sayen Denis Law da suka kai £155,000 a shekarar 1962.

Labarai masu alaka