Sunderland ta sayi 'yan wasan Man United

Image caption Paddy McNair da Donald Love

Kungiyar wasa ta Sunderland ta sayi 'yan wasan Manchester United na baya guda biyu a kan kudi £5.5m.

'Yan wasan dai su ne Paddy McNair da Donald Love kuma dukkannin su masu shekara 21, za su zauna a kulob din ne tsawon shekara hudu.

McNair wanda ya wakilci arewacin Ireland a gasar Euro 2016, ya fara bugawa Man United wasa a watan Satumba 2014, a inda ya taka leda har sau 27.

Shi kuma Donald Love wanda ya taka leda a kungiyar Wigan a kakar wasa da ta gabata, ya buga wa Man United din wasa sau biyu.

Kocin Sunderland, David Moyes ya ce " Ina son samun karin matasa kuma manyan 'yan wasa."

Labarai masu alaka