Ighalo ya tsawaita zamansa a Watford

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ighalo zai ci gaba da murza-leda a Watford zuwa shekara biyar

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Nigeria, Odion Ighalo, ya saka hannu kan ci gaba da taka-leda a Watford zuwa shekara biyar.

Dan kwallon mai shekara 27, ya koma Watford daga Udinese a shekarar 2014, inda ya taimaka mata samun tikitin shiga gasar Premier a kakar 2014-15.

Ighalo ya ci wa kungiyar kwallaye 17 a wasanni 42 da ya yi mata a kakar da aka kammala, wadda ta kare a mataki na 13 a Premier, sannan ta kai wasan karshe a kofin FA.

Watford za ta ziyarci Southampton a wasan farko a gasar Premier da za su kara a ranar Asabar.

Labarai masu alaka