West Ham United ta dauki aron Calleri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A mako mai zuwa Jonathan Calleri zai isa birnin Landan

West Ham United ta dauki dan kwallon tawagar Argentina, Jonathan Calleri aro daga Deportivo Maldonado ta Uruguay.

Dan wasan mai shekara 22, ya buga wa kasarsa tamaula wadda aka fitar a cikin wasannin rukuni a gasar kwallon kafa a Rio, zai kuma isa Landan a mako mai zuwa.

Calleri ya yi wata shida yana buga wa Sao Paulo ta Brazil aro, inda ya zama dan wasan da ya fi yawam cin kwallaye a Copa Libertadores.

West Ham za ta fara buga wasan farko a gasar Premier bana da Chelsea a ranar Litinin.

Labarai masu alaka