An dakatar da Pogba daga wasan farko

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paul Pogba, a lokacin da yake Juventus.

Sabon dan wasan da Manchester United ta saya da tsada, Paul Pogba, ba zai buga wasan da kulob din nasa zai taka da Bournmouth ba, ranar Lahadi.

An dai dakatar da Pogba ne daga wasan saboda samun Yalon kati guda biyu da ya yi, a kakar wasannin gasar Coppa Italia da ta gabata, lokacin yana kungiyar wasa ta Juventus.

Shi ma Chris Smalling na fuskantar dakatarwa kuma ba zai buga wasan ba.

Sauran sabbin 'yan wasan da Manchester United ta saya wato Zlatan Ibrahimovic da Henrikh Mkhitaryan da kuma Eric Billy za su taka leda, a wasan.

Labarai masu alaka