Leicester ta fara gasar Premier da kafar hagu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Leicester ce dai ta lashe gasar Premier da ta gabata.

Mai rike da kanbun gasar Premier ta bana Leicester City ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Hull City a wasan farko na gasar ta bana.

Hull ce ta fara zira kwallo a minti na 45 da fara wasan ta hannun Adama Diomande.

Riyad Mahrez ne ya rama wa Leicester da bugun fanareti bayan da aka kayar da dan wasan Najeriya Ahmed Musa, jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Robert Snodgrass ya kara zira kwallo ta biyu a ragar masu Leicester a minti na 57, abinda ya tabbatar musu da nasara.

Wannan ne karon farko a tarihi da aka doke masu rike da kanbun gasar a wasan farko tun 1989, lokacin da Arsenal ta sha kashi a hannun Manchester United.

Labarai masu alaka