Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa wannan domin sabunta bayanai

Image caption Ranar Asabar ake fara gasar Premier Ingila ta 2016-2017.

Barkanmu da ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa ranar Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya baki daya.

5:51 To sai ku ksance da sashen Hausa na BBC don jin yadda za ta kaya tsakanin Manchester City da Sunderland. A nan ne za mu gimtse shirin bayanai kai tsaye na labaran wasanni a wannan satin, da ftan za ku tara a mako mai zuwa.

5:34 Man City 1-0 Sunderland

5:30 An take wasa tsakanin Manchester City da Sunderland

5:05 Da karfe 5:30 ne Manchester City za ta kara da Sunderland

5:03 An kammala wasanni guda biyar.

4:41 Burnley 0-1 Swansea

4:35 Crystal Palace 0-1 West Brom

4:24 Everton 1-1 Tottenham

4:23 Southampton 1-1 Watford

3:52 Middlesborough 0-1 Stoke City

3:13 Southanmpton 1-0 Watford

3:10 Everton 1-0 Tottenham

2:56 Ita kuma Denmark ba ta ji dadin karonta da mai masaukin baki ba wato Brazil, a inda Brazil din ta ci ta hudu a wasan karshe na aji-aji.

2:55 Nigeria dai ta samu nasara a kan Japan da Sweden sai dai kuma Columbia ta lallasa ta da ci 2-0.

2:51 Idan an jima ne kuma Najeriya za ta fafata da Denmark a wasan dab-da-na-kusa-da-karshe

2:50 Har yanzu kuma Amurka ce a gaba da lambobin yabo 50

Hakkin mallakar hoto AFP

2:46 Ka da ku manta cewa ana can ana fafatawa a wasanni daban-daban a gasar Olympics da ake yi a birnin Rio

2:43 Wasannin da za a buga nan da wasu 'yan mintina

 • 3:00 Burnley vs Swansea
 • 3:00 Crystal Palace vs West Bromwich
 • 3:00 Everton vs Tottenham
 • 3:00 Middlesbrough vs Stoke City
 • 3:00 Southampton vs Watford
 • 5:00 Manchester City vs Sunderland

2:32 Teburin gasar Premier bayan wasa tsakanin Hull City da Leicester City

2:24 An tashi wasa tsakanin Hull City da Leicester City 2-1

2:14 Curtis Davies ya hana Jamie Vardy sakat

Hakkin mallakar hoto Getty

2:01 An ba wa Curtis Davies yalon kati saboda tade Shinji Okazaki

1:51 A minti 55 dan wasan Hull City, Robert Snodgrass ne ya zura kwallo ta biyu a ragar Leicester

1:44Hull City 2-1 Leicester City

1:19 Abel Hernandez ne ya ci wa Hull City ana gab da tafiya hutun rabin lokaci

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

1:16 Hull City 1-0 Leicester

12:50 Mahrez ya kai wani hari ragar Hull City

Hakkin mallakar hoto Getty

12:30 An take wasa tsakanin Hull City da Leicester City

12:25 'Yan wasan Hull City da matsayin da za su taka

12:23 Wannan shi ne wasan farko da Ahmed Musa, dan kwallon najeriya, zai fara bugawa Leicester a gasar Premier.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:21 'Yan wasan Leicester City da lambobin da za su taka.

12:14 Kasar Hungry ma ta samu lambar Azurfa ta hannun Laszlo Cseh kuma yanzu haka tana da lambobin yabo 11.

Hakkin mallakar hoto

12:12 Amurka ta samu cin azurfa ta hannun Michael Phelps kuma yanzu haka tana da jumillar lambobin yabo 50.

Hakkin mallakar hoto AFP

12:18 Shi ma dan wasan tsere na kasar Singapore, Joseph Schooling ya samu cin lambar yabo ta zinare wadda kuma ita ce lambar yabo ta farko da kasar ta samu a gasar.

Hakkin mallakar hoto

12:05 Dan wasan Linkaya na kasar Afirka ta Kudu, Chad Le Clos ya sami lambar yabo guda ta azurfa, abin da ya kawo wa kasar lambobin yabo 5 ke nan.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:52 Kafin a take wasa tsakanin Hull City da Leicester City, za mu leka kasar Bazil domin jin irin wainar da ake toyawa a gasar wasannin Olympics.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

11:47 Wasu daga cikin ra'ayoyin da kuke aiko mana ta shafukan sada zumunta

 • Aboubakar Roufai Filani: Tashin farko Arsenal ce a gaba kamun su dawo a wurinsu na 4 ,Liverpool za ta ba da mamaki a wannan shekarar, ita kuwa Leicester City za ta sha wahala da farko.
 • Jibrin Ummar Abbas Zaria: Toh Leicester City yau ce ranar da 'yar manuniya za ta nuna ko za ku iya kare gambunku na kofin Premier da kuka lashe, a bara, ko kuma a kasin haka, mu dai yau namu ido ne. Up Gunners!
 • Basheer Mukhtar Yusuf Zaria: Abin da ya faru a kakar wasan da ta gabata ya ba wa masana harkokin wasan kwallon kafa mamaki yadda Leiceter City ta iya kai bantanta har ta lashe gasar Premier League. To a wannan karo ina da tabbaci haka ba zai sake faruwa ba. Manchester United ce za ta cinye takarar.
 • Shu'aibu Idris Kofar-fada Bulangu: Toh Leceister City ku sani fa jiya ba yau ba ce, domin ba fa kullum ake kwana a gado ba, don haka muna fatan Hull city ta yi wuju-wuju da ku kamar da ci 2-0. Up Arsenal[
 • SaLeeh Muhammed SaLeeh Damare: Allah ya bawa mai rabo sa'a kawai zan ce domin wasannin bana kowa ya zo da haushin Leicester City ne.Up Barcelona!

11:38 Yayin da ake fara wasannin gasar Premier, sai ga shi sabon dan wasan Manchester United ba zai buga wasan ba.

An dakatar da Pogba daga wasan farko
Hakkin mallakar hoto Getty

11:34 Dan wasan Crystal Palace, Bolasie Yannick ya ce yana kyautata zaton Chelsea ce za ta dauki kofin Premier bana.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

11:31 Wasannin gasar Coppa-Italia na ranar Asabar

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 6:30 Udinese vs Spezia
 • 7:30 Novara vs Latina
 • 7:30 Pescara vs Frosinone
 • 7:30 Perugia vs Carpi
 • 7:30 Torino vs Pro Vercelli
 • 7:30 Chievo vs Virtus Entella
 • 7:30 Atalanta vs Cremonese
 • 7:30 Empoli vs Vicenza
 • 7:30 Cesena vs Ternana

11:18 Wasannin gasar Ligue 1 na Faransa na ranar Asabar

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 4:00 Bordeaux vs Saint-Étienne
 • 7:00 Montpellier vs Angers
 • 7:00 Dijon vs Nantes
 • 7:00 Caen vs Lorient
 • 7:00 Metz vs Lille

11:11 Wasannin gasar Championship na 13 ga Agusta

Hakkin mallakar hoto Reuters
 • 3:00 Aston Villa vs Rotherham United
 • 3:00 Barnsley vs Derby County
 • 3:00 Brentford vs Ipswich Town
 • 3:00 Burton Albion vs Bristol City
 • 3:00 Leeds United vs Birmingham City
 • 3:00 Newcastle United vs Huddersfield Town
 • 3:00 Preston North End vs Fulham
 • 3:00 Wigan Athletic vs Blackburn Rovers
 • 3:00 Wolverhampton vs Reading
 • 5:30 Norwich City vs Sheffield Wedn…

11:00 Gasar Premier Ingila mako na 1

Hakkin mallakar hoto PRESS ASSOCIATION
 • 12:30 Hull City vs Leicester
 • 3:00 Burnley vs Swansea
 • 3:00 Crystal Palace vs West Bromwich
 • 3:00 Everton vs Tottenham
 • 3:00 Middlesbrough vs Stoke City
 • 3:00 Southampton vs Watford
 • 5:30 Manchester City vs Sunderland

10:56 A shirimu na sharhi da bayanai gasar Premier, za mu kawo muku karawa tsakanin Hull City da Leicester City. Za mu fara gabatar da shirin da karfe 11:00 na rana agogon Nigeria da Nijar. Za ku iya bayar da gudunmawa a BBCHausa Facebook ko ta Twiiter ko kuma ta Google+ duk ta BBCHausa.

Hakkin mallakar hoto PA

Labarai masu alaka