Tottenham ta ƙwaci kanta daga Everton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Tottenham

Kungiyar wasa ta Tottenham ta kwaci kanta daga hannun Everton, bayan da suka tashi wasa 1-1.

Da farko dai sai Everton ce ta fara zargawa Tottenham kwallo a raga ta hannun Ross Barkley wanda ya doka bugun tazara.

Sai dai kuma dan wasan Tottenham, Erik Lamela ya farkewa kulob din nasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Tottenham ce dai ta zo ta uku a teburin gasar Premier da ta gabata.

Wannan dai shi ne wasan farko da kungiyoyin suka buga a gasar Premier bana.

Labarai masu alaka