Ba mu shirya wa gasar Premier ba - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal ta yi rashin nasara a wasanta na farko a gasar Premier bana a Emirates

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce bai sami isasshen lokacin kimtsa 'yan wasa ba, bayan Liverpool ta doke su 4-3 a wasansu na farko a gasar Premier a Emirates.

Wenger ya ce tun bayan da aka kammala gasar nahiyar Turai, bai yi atisaye da wasu 'yan wasansa ba, sannan da karancin kwarewa ga wasu.

Kociyan wanda 'yan kallo suka yi wa ihu ya ce "Wasu 'yan wasan da suka dawo sansanin horo ba su da kuzarin da za su taka mana leda".

Arsenal za ta buga wasa na biyu da Leicester City mai rike da kofin Premier, wadda ita ma ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Hull City a wasan farko

Labarai masu alaka