Chelsea za ta kara da West Ham United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasan farko da Antonio Conte zai jagoranci Chelsea a gasar cin kofin Premier

Chelsea za ta karbi bakuncin West Ham United a wasan farko a gasar Premier bana.

Chelsea wadda ke fatan taka rawar gani a wasannin shekarar nan, za ta iya fara karawar da sabbin 'yan wasan da ta sayo wato Michy Batshuayi da kuma N'Golo Kante.

Chelsea ta samu nasara a kan West Hama sau bakwai, sannan suka yi canjaras uku a wasanni 10 baya da suka yi.

Rabon da West Ham ta ci Chelsea a Stamford Bridge tun a watan Satumbar 2002, inda ta samu nasara da ci 3-2.

Labarai masu alaka