Bolt ya lashe tseren gudun mita 100

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Usain Bolt dan Jamaica ya yi ritaya daga yin tsere

Usain Bolt ya zama dan tseren gudun mita 100 na farko da ya ci lambar zinare a gasar Olympic uku a jere.

Bolt ya ci lambar zinariyar a Brazil a ranar Lahadi, inda ya kammala tseren mita 100 a dakika 9.81.

Dan wasan dan kasar Jamaica shi ne ya lashe tseren da aka yi a Beijin a shekarar 2008 da kuma wadda aka yi a Landan a 2012.

Gatlin dan kasar Amurka wadda sau biyu ana samunsa da laifin shan abubuwa masu kara kuzari shi ne ya yi na biyu a tseren.

Andre de Grasse na Canada ne ya ci lambar tagulla bayan da yi na uku a fafatawar.

Labarai masu alaka