Brazil ta doke Nigeria a kwallon kwando

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ce ta karshe a rukuni na biyu a gasar kwallon kwando a wasannin Olympic a Rio

Tawagar Brazil ta doke ta Nigeria da ci 86 da 69 a wasan kwallon kwando a gasar Olympic da ake yi a birnin Rio na Brazil.

Nigeria ce ta fara cin zangon farko da ci 16 da 15, ana shiga zango na biyu ne Brazil ta samu nasara da ci 27 da 15 sannan aka je hutu.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Nigeria ta ci karawar da 21 da 17, amma kuma a zangon karshe Brazil ta samu nasara da ci 27 da 17.

Nigeria wadda ta ci Croatia a rukuni na biyu, tasha kashi a hannun Argentina da Lithuania da Spaniya da kuma Brazil, tana mataki na karshe a teburi.

Labarai masu alaka