Chelsea ta ci West Ham United 2-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Antonio Conte yana murnar wasan da Chelsea ta fara ci a Premier

Antonio Conte ya fara gasar Premier bana da kafar dama, bayan da ya jagoranci Chelsea ta doke West Ham United da ci 2-1 a ranar Litinin.

Chelsea ce ta fara cin kwallo ta hannun Eden Hazard a bugun fenariti, bayan dan wasan West Ham Michail Antonio ya yi wa Cesar Azpilicueta keta.

James Collins ne ya farke kwallo a saura minti 23 a tashi daga karawar.

Daf da za a tashi daga wasan Diego Costa ya kara ci wa Chelsea kwallo na biyu, wanda hakan ya ba ta damar hada maki uku a fafatawar.

Chelsea za ta ziyarci Watford a wasa na biyu a gasar ta Premier a rana Asabar, yayin da West Ham United za ta karbi bakuncin Bournemouth a ranar Lahadi.

Labarai masu alaka