Rudisha ya kare kambunsa a tseren mita 800

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Rudisha shi ne ya lashe tseren mita 800 da aka yi a Landan a 2012

Dan kasar Kenya, David Rudisha, ya kare kambinsa, bayan da ya lashe tseren mita 800 a gasar Olympic da Brazil ke karbar bakuncin.

Rudisha mai shekara 27, ya lashe tseren ne a cikin dakika kasa da 43.

Dan kasar Algeria, Taoufik Makhloufi ne ya yi na biyu, yayin da Clayton Murphy na Amurka ya ci tagulla.

Rudisha shi ne ya ci lambar zinare a tseren mita 800 a gasar da aka yi a Landan a shekarar 2012.

Labarai masu alaka