An fitar da Enyimba a gasar zakarun Afirka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Enyimba tana mataki na bakwai a kan teburin gasar Firimiyar Nigeria

Al Zamalek ta ci Enyimba da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin zakarun Afirka da suka buga a Masar a ranar Litinin.

Zamalek ta Masar ta ci kwallon ne ta hannun Bassem Morsi a minti na 17 da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Enyimba ta Nigeria wadda ke da kofin na zakarun Afirka biyu ta buga wasanni uku ba ta samu nasara ba.

Da wannan sakamakon Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu da Al Zamalek sun kai wasan daf da na karshe a gasar bana a rukuni na biyu.

A rukunin farko kuwa Wydad Athletic Club ta Morocco da Zesco United ta Zambia ne suka kai wasannin daf da karshe a gasar.

Labarai masu alaka