Podolski ya daina bugawa Jamus tamaula

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Podolski tsohon dan wasan kungiyar Arsenal

Lukas Podolski ya sanar da cewar ya yi ritaya daga bugawa tawagar kwallon kafa ta Jamus tamaula.

Podolski mai shekara 31, wanda aka haifa a Poland ya bugawa Jamus wasanni 129, ya kuma ci mata kwallaye 48.

Yana kuma daga cikin 'yan wasan da suka daukarwa Jamus kofin duniya da aka yi a Brazil a shekarar 2014.

Podolski ya zauna a kan benci a karawar da Jamus ta doke Slovakia da ci 3-0 a gasar kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa a bana.

Dan kwallon wanda yanzu ke taka-leda a Galatasaray, ya yi wasa a FC Koln da Bayern Munich da kuma Arsenal.

Labarai masu alaka