Zan yi aiki da 'yan wasan Firimiyar Nigeria - Rohr

Hakkin mallakar hoto The NFF Twitter
Image caption Nigeria za ta kara da Zambia a ranar 3 ga watan Oktoba

Sabon kociyan tawagar Super Eagles, Gernot Rohr, ya ce zai yi amfani da kwararrun 'yan wasan da suke buga gasar Firimiyar kasar.

Rohr ya kalli karawar da 'yan wasan na Nigeria suka yi da Malaga da kuma Atletico a Spaniya, ya kuma ce ya gamsu da yadda suka murza-leda.

'Yan kwallon Nigeria sun yi rashin nasara a hannun Valenci da ci 2-1 da 4-1 da Malaga suka doke su da fafatawar da Atletico ta samu nasara da ci 1-0.

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria ta nada Gernot Rohr ne domin ya yi aiki tare da Salisu Yusuf, bayan da Paul Le Guen ya ki karbar aikin.

Nigeria tana rukuni da ya hada da Zambia da Kamaru da Algeria a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a shekarar 2018 a Rasha.

Labarai masu alaka