Olympic: An kora dan wasa gida kan kin gaisawa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Islam El Shehaby ya ki ya gaisa da abokin karawarsa

An kora mai wasan Judoka na Masar, Islam El Shehaby gida, bayan da ya ki gaisawa da abokin karawarsa Or Sasson dan Isra'ila bayan sun kammala wasa.

Tun da fari kwamitin Olympic na duniya ya ja kunnen dan wasan bisa halin da ya nuna, bayan da aka doke shi a zangon farko a karawar da suka yi a ranar Juma'a.

Kwamitin ya ce halin da El Shehaby ya nuna, baya cikin muradin karfafa zumunta tsakanin 'yan wasa a kundin da aka tanada na wasannin Olympic.

Kwamitin Olympic na Masar ya yi tir da halin da dan wasan ya nuna, sannan ya tasa keyarsa zuwa gida.

Bayan da El Shehaby zai fita daga fili, yan kallo sun yi ta yi masa ihu har zuwa barinsa filin wasa.

Labarai masu alaka