Wayde ya kafa sabon tarihi a Olympic

Hakkin mallakar hoto ALLSPORT GETTY

Ɗan wasan tsere na mita 400 dan ƙasar Afrika ta Kudu, Wayde van Niekerk, ya kafa sabon tarihi a gasar Olympics.

Wayde ya doke Micheal Johnson wanda ya kafa tarihi shekaru 17 da suka wuce, inda ya karbi lambar Zinare bana a gasar.

Matashin mai shekaru 24 ya kammala tseren ne cikin mintoci 43 da daƙiƙa uku, wato daƙiƙoƙi15 ƙasa da lokacin da Micheal Johnson ya kammala a shekarar 1999.

Grenada's Kirani James wanda ya lashe wasan a gasar Olympic din da aka yi a London shi ya zo na biyu kuma ya samu Azurfa, sai LaShawn Merritt dan Amurka wanda ya samu tagulla.

Micheal ya yi tsokaci game da Wayde 'Usain Bolt zai yi ritaya kwanan nan, Van Niekerk zai iya zama zakara a nan gaba.'

Labarai masu alaka