Conte ya kare Diego Costa kan ƙeta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lokacin da Diego Costa ya sari kaurin Adrian

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya ce rafali ya yi "abin da ya dace" da bai dauki mataki ba a kan dan wasan kulob din na gaba, Diego Costa sakamakon muguntar da ya yi wa golan West Ham, Adrian.

Shi dai Costa wanda yake da yalon kati guda, ya sari ƙaurin Adrian ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Rafalin, Anthony Taylor bai dauki wani mataki ba dangane da hakan, a inda kuma Costa ya zura kwallon da aka tashi wasa 2-1.

Conte ya ce Rafalin "bai ga abin da ya faru ba", "na ga Costa ya taka golan daga bisani kuma ya tsaya."

A ranar Litinin ne dai Chelsea ta kara da West Ham a wasan farko na gasar Premier Ingila.

Labarai masu alaka