An soke zinaren Rasha a tseren mita 100

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwamitin Olympic na duniya ya tsananta bincike kan amfani da abubuwa masu kara kuzari

Kwamitin Olympic na duniya ya soke lambar zinare da Rasha ta ci a tseren mita 100 na 'yan wasa hudu a gasar da aka yi a Beijin, a shekarar 2008.

Kwamitin ya yanke wannan hukuncin ne bayan sakamakon gwajin da aka yi wa Yulia Chermoshanskaya ya nuna, ta sha abubuwa masu kara kuzari.

Kimanin 'yan wasa 454 kwamitin ya saka a yi wa gwaji kan amfani da abubuwa masu kara kuzarin daga samfurin da ta dauka a gasar da aka yi a China.

Hakan na nufin Belgium wadda ta yi ta biyu a tseren ta koma ta daya, Nigeria kuma ta yi ta biyu, da kuma ta uku a karawar.

Kwamitin na Olympic na duba yi wu war dakatar da Chermoshanskaya, mai shekara 30, a tseren mita 200 wanda ta kammala a mataki na takwas.

Labarai masu alaka