Tsohon shugaban FIFA ya mutu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Joao Havelange dan kasar Brazil ne

Tsohon shugaban Fifa Joao Havelange ya mutu yana dan shekara 100.

Mutumin dan asalin kasar Brazil, wanda ya rike hukumar ta Fifa daga 1974 zuwa 1998, shi ne wanda Sepp Blatter ya gada.

Mista Joao ya yi murabus a matsayin shugaban Fifa na jeka-nayika a watan Afrilun 2013, bayan binciken badaklar cin hanci da ta mamaye hukumar.

A 2014 ne kuma a kwantar da shi a asibiti saboda fama da cutar huhu.

Havelange ne dan wasan da ya wakilci Brazil a gasar wasan kurme yayin gasar Olympics ta 1936.

Kuma a wannan shekarar ne ya zama lau kafin a zabe shi zuwa Kwamitin Olympic na Duniya.

Joao ne shugaban Fifa da ya mayar da kungiyoyin wasanni daga 16 zuwa 32 a gasar wasan Kwallon Kafa ta Duniya kuma an yi gasar har guda shida a zamanin shugabancinsa.

Labarai masu alaka