Golden Eaglets na atisaye a Sokoto

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption 'Yan wasan Golden Eaglets

'Yan wasan kungiyar wasa ta Golden Eaglets na Najeriya sun sauka a birnin Sokoto domin yin atasaye, a shirye-shiryen karawa da Junior Menas ta kasar Niger.

Wannan wasa ne dai na neman cancantar samun gurbin shiga gasar Zakarun Afirka ta AFCON.

Kocin kungiyar ta Golden Eaglets, Manu Garba ne dai yake jan ragamar tawagar da ta kunshi 'yan wasa 20.

A ranar Talata ne 'yan wasan za su cigaba da yin atasaye a filin wasa na Giginya.

Garba Manu ya ce "Muna tafe da 'yan wasa 20 amma kuma 18 ne kawai za su samu damar taka leda saboda haka za a samu gasa tsakanin 'yan wasan."

Labarai masu alaka