Tottenham: Lloris ba zai buga wasanni ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hugo Lloris ya samu raunin a lokacin wasansu da Everton

Golan Tottenham, Hugo Lloris ba zai sake buga wasa ba har tsawon mako hudu sakamakon raunin da ya samu a cinyarsa.

Hugo dai ya samu raunin ne a lokacin wasansu da suka tashi 1-1 da Everton, ranar Asabar.

Michael Vorm ne ya maye gurbin dan wasan wanda dan kasar Faransa ne, minti 35 da take leda, a filin wasa na Goodison Park.

Yanzu haka dai Lloris mai shekara 29 ba zai bugawa Tottenham wasannin da kulob din nasa zai kara da Crystal Palace da Liverpool da Stoke da kuma Sundeland.

Labarai masu alaka