Manchester City ta doke Steaua 5-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyoyin biyu za su kara a wasa na biyu a ranar Laraba a Ettihad

Manchester City ta casa Steaua Bucharest da ci 5-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.

David Silva ne ya fara cin kwallo, sai Sergio Aguero ya ci uku a karawar, sannan Nolito ya ci kwallo daya.

Aguero ya barar da fenariti biyu a fafatawar, ta farko da ya buga mai tsaron raga ne ya hanata shiga, ta biyu kuwa da ya buga ta yi fadi.

Manchester City tana buga wasan neman shiga gasar zaraun Turai ne, bayan da ta kammala a mataki na hudu a teburin Premier da aka yi.

Manchester City za ta karbi bakuncin wasa na biyu a ranar 24 ga watan Agusta a Ettihad.

Labarai masu alaka