Bolt ya kai daf da karshe a tseren mita 200

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Alhamis za a yi tseren mita 200 a zagayen daf da karshe

Usain Bolt ya kai zagayen daf da karshe a tseren mita 200, bayan da ya kammala fafatawar a cikin dakika 20.28.

Bolt wanda ya ci lambar zinare a tseren mita 100 a ranar Lahadi, ya karasa tseren mita 200 da sassarfa bayan da ya rage mita 50.

Sauran 'yan wasan da suka kai zagayen daf da karshe sun hada da 'yan wasan Birtaniya Adam Gemili da Danny Talbot da Nethaneel Mitchell-Blake da kuma dan Amurka Justin Gatlin.

A ranar Alhamis za a fafata a wasan daf da karshe, domin fitar da wadan da za su kara a wasan karshe.

Labarai masu alaka