Rio 2016: Oduduru ya je wasan kusa-da-karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Divine Oduduru tare da abokan wasansa a lokacin gasar tseren matasa na Afirka

Dan wasan gudun tsaren fanfalaki na Najeriya, Ejowvokoghene Divine Oduduru ya cancanci zuwa wasan kusa-da-na-karshe da za a yi ranar Laraba.

Divine dai ya zo na biyu bayan fitaccen dan tseren nan na Jamaica, Usain Bolt, a tseren mita 200 da suka yi da yammacin Talata.

Ejowvokoghene Divine Oduduru, mai shekara 19 ya lashe azurfa a gasar 2014 ta matasa.

Shi ne dan wasan da ya fafata har sau biyar a gasar tseren ta matasa na nahiyar Afirka.

Labarai masu alaka