Sweden ta fitar da Brazil a tamaular mata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sweden za ta kara da Jamus a wasan karshe a ranar Juma'a

Tawagar kwallon kafa ta Sweden ta mata ta cire ta Brazil daga gasar wasannin Olympic a bugun fenariti da ci 4-3.

Kasashen biyu sun tashi wasa ne babu ci, dalilin da ya sa ta kai su ga bugun fenariti, inda Sweden ta kai wasan karshe.

Sweden din za ta buga da Jamus wadda ta doke Canada a wasan daf da karshe da ci biyu a ranar Juma'a.

Brazil kuwa mai masaukin baki za ta buga wasan neman mataki na uku da Canada a dai ranar ta Juma'a.

Labarai masu alaka