West Ham ta kammala daukar Calleri aro

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea ta ci West Ham 2-1 a wasan farko a gasar Premier a ranar Litinin

West Ham United ta kammala daukar dan kwallon tawagar Argentina, Jonathan Calleri aro daga Deportivo Maldonado ta Uruguay.

Dan wasan mai shekara 22, ya buga wa kasarsa tamaula wadda aka fitar a cikin wasannin rukuni a gasar kwallon kafa a Rio.

Calleri ya yi wata shida yana buga wa Sao Paulo ta Brazil aro, inda ya zama dan wasan da ya fi yawan cin kwallaye a Copa Libertadores.

Dan wasan wanda ya taka-leda a Boca Juniors ya buga wasanni 90, inda ya ci kwallaye 39 a kakar wasanni biyu da ya yi.

Labarai masu alaka