Barcelona ta dauki Spanish Super Cup

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Juma'a za a fara gasar cin kofin La Liga a Spaniya

Barcelona ta dauki Spanish Super Cup bayan da ta doke Sevilla da ci 3-0 a karawar da suka yi a Camp Nou ranar Laraba a wasa na biyu.

A wasan farko da suka buga a ranar Lahadi Barcelona ce ta ci 2-0, jumulla ta doke Sevilla gida da waje 5-0.

Wannan shi ne karon farko da Barcelona ta ci Spanish Super Cup tun wanda ta dauka a 2013.

Hakan kuma na naufin za a fara gasar La Liga ta bana a ranar Juma'a, a ranar Asabar Barcelona za ta kece raini da Real Betis a gida.

Ita kuwa Sevilla za ta karbi bakuncin Espanyol ce.

Labarai masu alaka