Jamus ta doke Nigeria da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria za ta kara da Honduras a ranar Juma'a a neman mataki na uku

Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Nigeria ta maza ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Jamus a ranar Laraba.

Kasashen biyu sun fafata ne a wasan daf da karshe a gasar kwallon kafa a wasannin Olympic da ake yi a Brazil.

Jamus ta ci kwallon farko ta hannun Lukas Klostermann a minti tara da fara wasa, sannan Nils Petersen ya kara ta biyu daf da za a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Jamus ta kai wasan karshe za kuma ta kara da Brazil wadda ta ci Honduras 6-0.

Nigeria kuwa za ta kece raini a wasan neman mataki na uku da Honduras.

Labarai masu alaka