Joe Hart na tunanin barin Manchester City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Joe Hart ya koma Manchester City da taka-leda a 2006

Joe Hart na tunanin barin Manchester City, bayan da sabon koci Pep Guardiola ya ki saka shi a wasanni biyu a jere.

Tuni Everton da kungiyar Sevilla mai buga gasar La Ligar Spaniya suka nuna sha'awar sayen mai tsaron ragar.

Hart mai shekara 29, na son komawa wata kungiyar aro domin ya gwada kwarewarsa, duk da saura makwonni biyu a rufe kasuyar saye da sayar da masu buga tamaula.

Ana kuma rade-radin cewar 'yan wasan Barcelona Marc-Andre ter Stegen da kuma Claudio Bravo za su koma Ettihad da taka-leda.

Hart ya bugawa Ettihad wasanni kusan 350 a dukkan fafatawar da ya yi wa kungiyar, tun komawarsa can daga Shrewsbury a shekarar 2006.

Labarai masu alaka