Pillars ta ziyarci Nasarawa United

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Twitter
Image caption Karawar farko da Pillars ta ci Nasarawa United 2-1 a jihar Kano

Nasarawa United za ta karbi bakuncin Kano Pillars a wasan karshe na mako na 31 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria da za su kara a ranar Alhamis.

A wasan farko da suka yi a cikin watan Afirilu, Kano Pillars ce ta doke Nasarawa United da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

A ranar Laraba Sunshine ta ci Ikorodu United 3-0 a wasan mako na 31, yayin da Shooting Stars da El Kanemi Warriors suka tashi canjaras.

Ga sakamakon wasannin mako na 31 da aka yi:
  • Sunshine Stars 3-0 Ikorodu Utd
  • 3SC 0-0 El-Kanemi
  • Rivers Utd 1-0 Heartland
  • Ifeanyiubah 2-0 Rangers
  • MFM 1-1 Wolves
  • Lobi 3-2 Abia Warriors

Labarai masu alaka