Mahrez ya tsawaita zamansa a Leicester

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Leicester ta yi rashin nasara a hannun Watford da ci daya mai ban haushi a wasan farko a Premier

Riyad Mahrez ya saka hannu kan ci gaba da taka-leda a Leicester City mai rike da kofin Premier zuwa shekara hudu.

Dan wasan tawagar Algeria, mai shekara 25, an yi ta rade-radin cewar zai koma Arsenal da muza-leda a baya can.

Mahrez ya ci kwallaye 17 ya kuma bayar da kwallo aka ci a raga sau 11, kuma shi ne kwararrun 'yan wasan tamaula suka zaba a matakin wanda ya fi fice a gasar da aka yi.

Dan kwallon ya bi sahun Wes Morgan da Jamie Vardy da Kasper Schmeichel da kuma Andy King a matsayin wadan da suka sabunta kwantiraginsu da Leicester City.

Mahrez ya koma Leicester City a watan Janairun 2014 daga Le Havre.

Labarai masu alaka