Bolt ya kai wasan karshe a tseren mita 200

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Bolt ya lashe tseren mita 100 kuma karo na uku a jere a gasar Olympic

Usain Bolt ya kai wasan karshe a tseren mita 200 a wasannin Olympic da ake yi a Brazil.

Bolt dan kasar Jamaica, wanda ya ci lambar zinare a tseren mita 100, na fatan lashe lamabar zinare a tseren mita 200 wadda ya ci a Landan a 2012.

Dan Nigeria Ejowvokoghene Oduduru ya kasa kai wa wasan karshen, bayan da ya kammala a mataki na bakwai a tseren samun gurbi da ya yi.

A ranar Alhamis ake sa ran yin wasan karshe a tseren mita 200.

Labarai masu alaka