Andre Ayew zai yi jinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Ham ta sayo Ayew daga Swansea a bana

Dan wasan West Ham United, Andre Ayew zai yi jinya, bayan raunin da ya yi a karawar da Chelsea ta ci West Ham a gasar Premier a ranar Litinin.

Ayew dan kwallon tawagar Ghana, mai shekara 26, ya buga minti 35 a wasan farko da ya buga wa West Ham, daga baya aka fitar da shi daga karawar.

West Ham United ta sanar da cewar ,ba ta san ranar da dan wasan zai murmure ba, bayan da ta auna girman raunin da ya yi.

Ta kuma ce ya yi wuri ta sanar da ranar da Ayew zai dawo daga jinya, domin ya ci gaba da murza mata leda.

Labarai masu alaka