Ayew zai yi jinyar watanni hudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Ham za ta kara da Bournemouth wadda United ta ci 3-0 a ranar Lahadi

Dan wasan West Ham United, Andre Ayew, zai yi jinyar watanni hudu, bayan raunin da ya yi a karawar da Chelsea ta ci West Ham a gasar Premier a ranar Litinin.

Ayew dan kwallon tawagar Ghana, mai shekara 26, ya buga minti 35 a wasan farko da ya yi wa West Ham, daga baya aka fitar da shi daga karawar.

West ham ta sayi Ayew daga Swansea kan kudi sama da fan miliyan 20.

West Ham za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasa na biyu na gasar cin kofin Premier ranar Lahadi 21 ga watan Agusta.

Labarai masu alaka